BrocoliCourtois2480010
B
BrocoliCourtois2480010
Ses blogs
Articles :
43
Depuis :
23/02/2018
Categorie :
Marketing & Réseaux Sociaux
Articles à découvrir
A jamhuriyar nijar, yau ne 24 ga watan afrilu ake gudanar da bikin ranar hadin-kan ‘yan kasa, ranar da ta samo asali daga yarjejeniyar zaman lafiya ta farko da aka kulla tsakanin ‘yan tawaye da gwamnatin kasar a irin wannan ranar ta shekarar 1995. an dai kulla yarjejeniyar ce a lokacin tsohon shugaban kasar marigayi janar ibrahim ba’are maina
A wata sanarwa dake yawo kan shafukan sada zumunta babban hafsan sojin kasar ta nijar, ya sanya wa hannu, anyi wa birgediya janar mahamadou mounkaila ritaya, daga ranar 19 ga watan afrilu saboda rashin da’a. sanarwar ta kuma ce an kore shi daga duk wani aikin soji daga ranar.
Mahukunatn a birnin yamai, sun kafa dokar hana bara, da kuma baiwa mabarata sadaka a kan tituna. daga ranar 1 ga watan mayu, 2019 duk wani da aka samu kan titi yana bara to zai gamu da fishin hukuma, inji sanarwar da mahukuntan birnin na yamai suka fitar. an amince da dokar ce bayan wani taron tattaunawa da bangarori daban daban na al'umma inda dag
Nijar ta lashe kofin kokowar garjiya ta cedeao a côte d’ivoire
A yayin kwambalar da aka kammala ranar lahadi, 21 ga watan afrilu 2019 a birnin bouake, dan wasan kokowa # abdoulaye_salam daga nijar, ya lashe kofin. kwambalar ta kasashe mambobi kungiyar #cedeao ta samu halartar kasashen da suka hada côte d’ivoire mai masabkin baki da mali da nijar da togo da burkina faso da kuma senegal. nijar ta samu matsayi
Nijar : mutum 3.331 suka mutu sanadin zazzabin cizon sauro a shekara 2018.
Ministan kiwon lafiya na kasar ne ya bayyana hakan a cikin jawabinsa na ranar yaki da cutar ta malaria da aka gudanar jiya 25 ga watan afrilu a duk fadin duniya. cutar wacce ita ce a sahun gaba wajen kisa a kasar ta kuma kama mutum 2.756 065 a cikin shekara data shude. a cewar ministan lafiya na nijar, dakta illiasu idi mai nasara, yara ‘yan kasa
Makamashi, ilimi, kiwan lafiya, samar da aiki, ruwa, da dai saurensu, su ne bangarorin da tsohon shugaban kasar nijar, alh. mahamane usman ya bayyana cewa yana da kyau ayi hulda dasu da kasar rasha. mahamane usman ya bada misali da matsalar ruwa da nijar, ke fama dasu, yin hulda da rasha a wannan bangaren zai magance matsalolin da al’umma ke fama
#nijar : majalisa ta amince wa gwamnati nadin shuwagabannin jami'o'i :
Ta faru ta kare, majalisar dokokin jamhuriya nijar, ta amince da gagarimin rinjaye da kudrin da gwamantion ta gabatar mata na neman nada shuwagabannin jami'o'in gwamnati. 'yan majalisa 135 ne suka amince da kudirin, a yayin da 28 suka ki amincewa, sai kuma 2 da sukayi rawar kuri'arsu. wanann ya sanya daga yanzu gwamnatin kasar ce zata nada shugaban
Iyayen daliban da sukayi zanga zanga sun biya miliyan 7,3 na cfa
Babban mai shigar da kara na gwamnatin nijar, ne ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai, game da barnar da dalibai sukayi yayin wata zanga zanga a ranar 9 ga watan afrilun nan. a yanzu an salami dukan daliban da ake tsare da, bayan da iyayensu suka biyar kudadden barnar da akayi. a yayin taron manema labaren, mai shigar da kara na gwamn
Wata mahardaciyar al'kur'ani mai girma ta sake haska sunan nijar a idon duniya. malama fatima ussaini musa, wacce ta wakilci nijar a gasar al'kur'ani mai girma ta ciri tuta inda ta zo a matsayi na farko a musabakar da aka gudanar a kasar malaisiya.
Rahotanni daga yamai na cewa mutane kimanin 55 ne suka kone kurmus a daren jiya lahadi wayewar wannan safiya ta litinin bayan da wata tankar mai ta jirkice, ta kuma kama da wuta. wasu rahotanni na daban na cewa adadin ya haura hakan. shugaba isufu mahamadu ya jajantawa iyalen wadanda hatsarin fashewar tankar mai ya rusa dasu.